Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Adamawa ya yi Murabus

 

Adamawa – Rikicin da ke faruwa a jam’iyyar All Progressives Congress, APC, reshen jihar Adamawa ta janyo shugaban jam’iyyar, Alhaji Ibrahim Bilal ya yi murabus.

Ya mika wasikar murabus dinsa nan take, a cewar wani rahoto na The Nation.

Murabus din Bilal na zuwa ne a yayin da ake samun rashin jituwa tsakaninsa da Kwamitin Ayyuka na jam’iyyar.

Majiyoyi daga cikin jam’iyyar sun ce ta yi wu an bashi shawarar yin murabus ne bayan an zarge shi da hada kai da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar hammaya da wasu abubuwan.

Amma, cikin wasika mai dauke da kwanan wata na 13 ga watan Satumban 2022, da Bilal ya rubutawa shugaban APC na kasa, Sanata Abdullah Adamu ta hannnun Kwamared Mustapha Salihu, mataimakin shugaban jam’iyya na kasa, shiyyar arewa maso gabas, Bilal bai bayyana dalilin murabus dinsa ba.

Kawai ya ce ya yi murabus ne nan take.

Dakaci karin bayani …

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here