Kisan Mahauta 7 ‘Yan Arewa: Shugaban Hausawa a Jahar Imo ya Wanke ‘Yan Kungiyar IPOB

 

Wani shugaban Hausawa a jahar Imo ya karyata zargin da ake yiwa kungiyar IPOB da kisan Hausawa.

Ya siffanta kisan Hausawa mahautan 7 da rikicin siyasa da kuma shirin tunzura ‘yan Arewa.

Hakazalika ya bayyana cewa ‘yan siyasa ne ke rura wutar rikici don raba al’ummar Ibo da Hausawa.

Mataimakin ko’odinetan al’ummar Hausawa a jahar Imo, Sulaiman Ibrahim Sulaiman, wanda aka fi sani da Garkuwan Hausawa, ya yi magana a wata hira da jaridar Punch game da kisan wasu mahauta bakwai a jahar da wasu ‘yan bindiga suka yi.

Sulaiman ya bayyana cewa, babu shakka kisan Hausawan bakwai wani yunkuri ne na ta da zaune tsaye, musamman ma fada ta kabilanci, yana mai nuna takaicin irin wannan aika-aikata tare da mika wuya ga kaddarar Allah.

Da aka tambayeshi dangane da abinda ya fahimta a matsayin dalilin da yasa ‘yan bindigan suka kashe mahautan, Sulaiman ya ce: “Kashe-kashen na da nasaba da siyasa.

Ba shi da wata alaka da ‘Yan asalin Biafra ko kungiyar tsaro ta Gabas.

“‘Yan siyasan da suka fusata, wadanda ba sa farin ciki da sauye-sauyen da ke faruwa a jahar Imo, su ne suka kitsa kashe-kashen.

“Suna son mayar da jahar Imo mara dadin mulki ga fitaccen sanata Hope Uzodinma, amma da yardar Allah, ba zasu taba yin nasara ba.

Ya kuma bayyana cewa, maharan sun afkwa al’ummar Hausawa ne saboda ‘yan Arewa su tunzura su fara fada al’ummar Ibo da ke zaune a yankunan Arewa.

Sulaiman ya kuma wanke kungiyar IPOB da ake zargin su suka kai wa Hausawan hari, in da yake cewa,: “Masu kisan suna kokarin nuna kamar kungiyar IPOB ce ta shirya kisan, amma ba IPOB ba ce; kashe-kashen na da alaka da siyasa.

Wadanda suke yiwa Gwamnatin jahar Imo mummunan fata ne suka dauki nauyin wadanda suka yi kisan.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here