ƙalubalen Tsaro da Gwamnatin Yanzu ke Fuskanta Bazai sa Ace ƙasar ta Lalace ba – Shugaban Majalisar Dattijai

 

Shugaban majalisar dattijai, Sanata Ahmad Lawan ya ce babu yadda za’ai Najeriya ta faɗi, ta lalace a yanzun tunda har bata lalace a zamanin mulkin Jonathan ba.

Lawan ya yi wannan jawabi ne a wajen ƙaddamar da shirin koyon sana’a da kuma samar da aikin yi a mazaɓar sanatoci ta Katsina ta tsakiya.

Ya ƙara da cewa bazai taɓa yuwu wa wai saboda matsalar tsaron da muke fama da ita ace Najeriya zata lalace ba, shin mun mance ne da lokacin da aka sa dokar ta baci a yankin arewa maso gabas Shugaban majalisar dattijai, Sanata Ahmad Lawan, ya ce ƙalubalen tsaro da gwamnatin yanzun ke fuskanta bazai sa ace ƙasar ta lalace ba.

Lawan ya faɗi haka ne a ya yin da yake ƙaddamar da shirin samar da aikin yi wanda mutane 2000 suka amfani dashi a mazaɓar Katsina ta tsakiya.

A watan Disamban shekarar data gabata, jaridar Financial Times ta bayyana cewa Najeriya na kan hanyar wargajewa.

Jaridar kasuwancin ta ƙasa-da-ƙasa ta ƙara da cewa ƙalubalen tsaro da ƙasar ke fama dashi ya tsayar da cigaban tattalin arziƙinta wanda wannan babban ƙalubale ne kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Hakanan a ranar Jumu’an da ta gabata, ƙungiyar gwamnonin jam’iyyar hamayya ta PDP, ta ce Najeriya na tafiya a hankali zuwa lalacewa matuƙar wannan matsalolin rashin tsaron ya cigaba da faruwa.

Amma shugaban Sanatocin ya ce duk masu irin wannan tunanin “Sun manta da halin da ƙasar ta baro ne.”

Lawan ya ce “Najeriya bata lalace ba a lokacin mulkin tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan, saboda haka bazai yuwu ta lalace a yanzun ba.”

“Duk waɗanda ke cewa wannan yanayin da muke ciki na rashin tsaro zai sa ƙasar nan ta lalace, ta wargatse, ko kuma tana kan hanyar hakan, to lallai sun manta abunda ya faru a baya ne. Najeriya ba zata taɓa wargatsewa ba. Hakanan kum shugaban sanatocin ya ce, idan sun mance ne to su tuna cewa a zamanin GEJ ne aka saka dokar ya ɓaci a yankin arewa maso gabas.”

“Amma Najeriya bata lalace ba, sabida haka a yanzun ma ba zata lalace ba.” Inji Ahmad Lawan.

Mutum mai daraja ta uku a ƙasar nan ya yi kira ga duk masu ruwa da tsaki da su haɗa karfi da ƙarfe da gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari wajen ƙanin an yaƙi matsalar tsaro ta yaƙi ci yaƙi cinyewa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here