Yadda Shugaban Kamfanonin Mai a Rasha ya Kashe Kansa

An samu shugaban daya daga cikin manyan kamfanonin mai a Rasha Lukoil, a mace a Moscow.

Kafar yada labaran Rasha ta ce Ravil Maganov, ya fado ta taga daga hawa na shida a wani asibiti.

Rahotanni sun rawaito cewa masu bincike sun ce dalilin mutuwar mutumin shi ne ya kashe kansa da kansa.

A watan Maris, daraktoci a hukumar gudanarwar kamfanin man suka nuna damuwa a game da yakin da ake a Ukraine, sannan kuma suka yi kira da a samu a yi sulhu.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here