Shugaban Kasar Nijar ya Magantu Kan Yakin Iran da Isra’ila

 

Niamey, Nijar – Shugaban kasar Nijar, Janar Abdourahaname Tchiani ya tsoma baki game da yakin da ake yi a Gabas ta Tsakiya.

Tchiani ya nuna damuwa game da yakin da ake yi tsakanin Iran da Isra’ila da ke samun goyon bayan Amurka.

Shugaban Tchiani ya bayyana haka yayin wani taro da aka gudanar wanda tashar RFI Hausa ta ruwaito.

Shugaban Tchiani ya bayyana haka yayin wani taro da aka gudanar wanda tashar RFI Hausa ta ruwaito.

Yadda yakin iran da Isra’ila ya barke

Wannan na zuwa ne bayan yaki ya barke a Gabas ta Tsakiya tsakanin Iran da kuma kasar Isra’ila.

Amurka da Isra’ila ne suka fara kai harin ne a ranar 28 ga watan Fabrairun shekarar 2026 da muke ciki wanda ya sanadiyyar rayuka da dama.

Yayin harin, jagoran addini a Iran, Ayatollah Ali Khamenei ya rasa ransa da wasu manyan jami’an tsaro a kasar.

Daga bisani, Iran ta mayar da martani inda ya ci gaba da harba makaman rokoki wanda ya jawo asara ga bangaren Amurka da Isra’ila.

Abin da Tchiani ya ce kan yakin Iran/Isra’ila

Yayin jawabinsa, Tchiani ya yi zargin cewa ana kulla manakisa kan farmaki a Nijar, Mali da Burkina Faso domin biyan bukatar wasu kasashe.

Shugaban ya ce wasu ƙasashe na neman yin amfani da damar yakin da ake yi domin afakawa Nijar.

Ya ce:

“Ba zan kammala wannan jawabi ba sai na tabo batun yankin Gabas ta Tsakiya da wasu kasashe da ke fama da yaki.

“Wannan lamari dai yana daga mana hankali matuka musamman tattalin arzikinmu, yana daga mana hankali saboda yana shafar yan uwanmu.”

Shugaban ya ce ya zama wajibi kasashensu su koyi darasi game da abin da ke faruwa, ka da su manta akwai manyan kasashe da dama masu mummunanr manufa.

“Za su iya amfani da wannan dama domin kaddamar da hare-hare a kan kasarmu, zan yi amfani da wannan dama domin kara jinjinawa al’ummarmu saboda tsayawa tsayin daka domin yaki da wannan mummunan manufa.

“Ba za mu taba bari makiya su zo su bata mana kasa ba, za mu karfafa kungiyar kasashenmu ta AES domin kare kai daga duk abin da zai cutar da mu.”

– Abduorahamane Tchiani

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here