Shugaban Kungiyar NUT ya Zama ‘Dan Takarar Gwamna a Jihar Kebbi

 

Shugaban kungiyar NUT, Nasiru Idris APC ta tsaida a matsayin ‘dan takarar Gwamnan jihar Kebbi.

Kwamred Nasiru Idris zai rikewa jam’iyyar APC mai mulki tuta a zaben 2023, zai gwabza da PDP.

Idris ya doke Sanata Yahaya Abdullahi wanda suke rigima da bangaren Gwamna Atiku Bagudu a APC.

Kebbi – Shugaban kungiyar NUT ta malaman makaranta, Nasiru Idris, ya zama ‘dan takarar gwamnan jihar Kebbi a karkashin jam’iyyar APC.

Jaridar The Cable ta ce Nasiru Idris ya doke Sanata Yahaya Abdullahi da Abubakar Gari-Malam wajen samun tikitin APC mai mulki na jihar Kebbi.

A halin yanzu, Sanatan Yahaya Abdullahi shi ne shugaban masu rinjaye a majalisar dattawa.

A ranar Alhamis, 26 ga watan Mayu, 2022 Idris Yahuza ya bada sanarwar sakamakon zaben tsaida gwanin, ya ce Abdullahi bai samu kuri’a ko daya ba.

A cewar malamin zaben, Malam Nasiru Idris ya samu kuri’u 1, 055 a cikin 1, 090 da aka kada, shi kuma Malam Gari-Malam ya tashi da ragowar kuri’u 35.

Nasiru Idris ya yi murna

Rahoton da ya fito daga hukumar dillacin labarai na kasa ya tabbatar da cewa Idris ya yi farin cikin samun nasarar zama ‘dan takarar gwamnan APC.

Idris ya yabawa masu ruwa da tsaki na jam’iyyar ta APC mai mulki da suka iya gudanar da zaben fitar da ‘dan takarar ba tare da an samu wata rigima ba.

Haka zalika ‘dan takarar gwamnan ya jinjinawa ‘ya ‘yan jam’iyyar da suka kada kuri’a a zaben.

The Cable ta ce baya ga zamansa shugaban kungiyar NUT na kasa, Idris shi ne mataimakin shugaban kungiyar kwadago watau NLC na Najeriya.

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here