Shugaban Jam’iyyar PDP ya Kalubalanci Mambobin Jam’iyyar Kan Batun ya yi Murabus
A karshe shugaban jam’iyyar PDP, Prince Uche Secondus ya magantu a kan neman da wasu mambobin jam’iyyar ke yi na yayi murabus.
Secondus ya bayyana cewa shi ba zai sauka daga mukamin nasa ba.
Ya kalubalanci masu kiran da su fito fili su bayyana laifin da ya aikata wanda yasa suke neman ya sauka daga mukamin.
Shugaban jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) na kasa, Prince Uche Secondus ya bayyana cewa ba zai yi murabus ba.
Ya ce ya kamata ‘yan tsirarun da ke kira da ya yi murabus su fito fili su bayyana laifin da ya aikata, jaridar The Nation ta ruwaito.
Shugaban PDP na kasa ya karya shirunsa a cikin wata sanarwa a Abuja ta hannun mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Mista Ike Abonyi, jaridar Punch ta ruwaito.
Sanarwar ta ce
“Shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Prince Uche Secondus ya ce ba zai yi murabus daga mukaminsa ba.
Read Also:
“Prince Secondus ya ce a cikin wata gajeriyar sanarwa daga ofishin yada labaransa cewa zuwa yanzu babu wani abu da ya ba da damar murabus dinsa daga mukamin jam’iyyar kuma wadancan ‘yan tsiraru da ke kira da ya yi murabus ya kamata su fito fili su fada wa membobin jam’iyyar a duk fadin kasar laifin da ya sa ake neman ya yi murabus.
“Ya ce zai ci gaba da mai da hankali tare da jajircewa kan manufofin jam’iyyar wanda ya lashi takobin karewa yayin zabensa don jagorantar wannan babbar jam’iyyar a watanni 44 da suka gabata.”
Ba ma bukatarka kuma: Yan majalisa na PDP sun nemi Secondus ya yi murabus a matsayin shugaban jam’iyyar
A baya, mun ji cewa masu ruwa da tsaki na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a majalisar wakilai sun nemi shugaban jam’iyyar na kasa, Uche Secondus, da yayi murabus daga mukaminsa.
Mambobin kungiyar masu ruwa da tsakin, a cikin wata sanarwar da shugabanta, Kingsley Chinda (PDP, Ribas) da Mataimakinsa, Chukwuka Onyema (PDP, Enugu) suka sa hannu, sun yi wannan kiran ne bayan wata ganawa da suka yi a ranar Asabar.
Sun dora alhakin matsalolin da ke faruwa a jam’iyyar a kan “halayar jagoranci” na Mista Secondus.