Shugaban Jam’iyyar PDP na Abuja ya Rasu

 

Shugaban jam’iyyar PDP na babban birnin tarayya Abuja ya rasu a wani haɗarin mota.

Sunday Zakka wanda yake cikin motarsa Peugeot ƙirar 406 ya yi haɗarin ne tare da mai gadinsa da matuƙinsa, kuma rahotanni na cewa nan mutum biyu suka mutu a cikin motar.

Haɗarin ya faruy ne da misalin ƙarfe 3:30 na dare lokacin da yake kan haryarsa ta koma gidansa da ke Kuje daga cikin garin Abuja.

An garzaya da shi asibitin koyarwa da ke Gwagwalada amma daga baya aka mayar da shi babban asibiti na ƙasa da ke cikin garin Abuja, inda kuma a nan ne rai ya yi halinsa.

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP Atiku Abubakar ya aike da saƙon ta’aziyya kan mutuwar shugaban na PDPn Abuja.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here