Real Madrid: Shugaban Kungiyar ya Kamu da Cutar Corona

 

Florentino Perez, shugaban kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ya kamu da corona.

Kungiyar ta sanar da hakan ne cikin wani sako da ta fitar a ranar Talata.

Sanarwar ta ce amma a halin yanzu baya nuna alamun cutar ta corona.

Shugaban kungiyar kwallon kafa na Real Madrid Florentino Perez mai shekaru 73 ya kamu da cutar covid 19 kamar yadda kungiyar ta sanar a ranar Talata, The Punch ta ruwaito.

Kungiyar da ke rike da kofin kwararru na kasar Spain cikin sanarwar da ta fitar ta ce Perez “baya nuna wasu alamun cutar a halin yanzu.”

An gano cewa Perez na dauke da cutar ne bayan mai horas da yan wasar kungiyar ta Real Madrid, Zinedine Zidane shima ya kamu da cutar a makon da ta gabata.

Zidane shima baya nuna alamun cutar kuma ya dawo filin horas da yan wasa na Madrid a safiyar ranar Talata bayan ya kebe kansa na wasu kwanaki.

Perez yana wa’adinsa na biyu a matsayin shugaban kungiyar Real Madrid wacce ta fara daga shekarar 2009. Shine kuma ya kula da kungiyar daga 2000 zuwa 2006.

Sanarwar ta ce: “Real Madrid ta tabbatar da cewa shugaban mu Florentino Perez ya kamu da kwayar cutar COVID19 dama an saba yi masa gwajin lokaci zuwa lokaci, duk da cewa baya nuna wasu alamu.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here