Shugabannin Kasashen da ke Mambobin NATO Sun Isa Birnin Brussels Domin Taron ƙoli Kan ƙasar Ukraine
Shugabannin kasashen da ke mambobin kungiyar tsaro ta Nato sun isa birnin Brussels domin duba matakan da suka dace su dauka domin mayar wa Rasha martani kan mamayar da ta ke yi a Ukraine.
Read Also:
Mambobin ƙungiyar sun dauki hoto tare, kamar yadda suka saba gabanin fara taron, wanda ake cewa yana cikin tarurruka mafi muhimmanci a tarihin kungiyar.
Yakin na Ukraine ya shiga wata na biyu ke nan tun bayan da Rasha ta tura dakarunta cikin kasar domin ta hana ta shiga kungiyar ta Nato da kuma zama mamba a tarayyar Turai, wadanda ke cikin wasu bukatu da Rashar ta bayyana a matsayin dalilinta na mamaye kasar.