Manyan Shugabannin Boko Haram na Aika mu a Kashe mu a Fagen Daga – Tsohon Kwamandan Boko Haram, Adamu Rugurugu

 

Wani kwamandan Boko Haram ya bayyana illolin da ya fuskanta lokacin da yake dajin Sambisa.

Ya bayyana cewa, kungiyar Boko Haram ba komai bane face zamba, kuma ana amfani da su ne a kashe su.

Ya ce, shugabannin Boko Haram matsorata ne ba sa shiga fagen daga a gwabza yaki dasu ko sau daya.

Wani tsohon kwamandan ‘yan ta’addan Boko Haram, Adamu Rugurugu, ya ce ya yi watsi da ta’addanci ne sakamakon gano cewa akidar ‘yan ta’addan Boko Haram zamba ce.

A cikin bidiyon da PRNigeria ta samu, kasurgumin dan ta’addan ya ce manyan shugabannin kungiyar a koyaushe za su aika su a kashe su ne a fagen daga, tare da yaudarar su cewa aljanna ce za ta zama makomar su idan an kashe su.

A cewar Mista Rugurugu, manyan shugabannin Boko Haram ba sa iya tunkarar sojoji sai dai buya daga baya suna amfani da mayakansu wajen kai hare-haren kan sojoji a arewa maso gabas.

Mista Rugurugu ya kuma yi wa sojojin Najeriya addu’ar nasara, tare da hada wa da sau la’antar wadanda ba sa son zaman lafiya a Najeriya.

Ya ce:

“… Sojojin da ke tausaya mana ba tare da cin zarafi ko musguna mana ba, muna addu’ar Allah ya kara musu daraja. Duk wanda zai kawo tashin hankali a Najeriya da kuma wanda baya son zaman lafiya ya wanzu, Allah ya nisanta shi da mu gaba daya.”

Ya kuma shawarci sauran ‘yan Boko Haram da ke daji da cewa, su mika kansu ga sojoji zai fi musu alheri, inda yake cewa:

“Ni da kaina, ga ‘yan uwana da har yanzu suke cikin daji, mun zabi mu aje makamai mu kuma mika kanmu don samun zaman lafiya.

“Ya kamata ku zama masu rikon amana, kowa zai yaba muku kuma gwamnati tana cika alkawuran da ta dauka, suna kula kan komai, duk wanda bai tuba ya gyara halayensa ba, tabbas za a dauki mataki a kansa.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here