Sifeto Janar na ‘Yan Sanda ya Karbi Rahoton Binciken Abba Kyari
Bayan makonni da kafa kwamitin bincike, an kammala binciken Abba Kyari .
Shugaba kwamitin ya mika takardun sakamakon binciken ga Sifeto Janar.
IGP Alkali ya yi alkawarin tabbatar da cewa an yi gaskiya da adalci.
Abuja – Labarin dake shigo mana da duminsa na nuna cewa an kammala bincike kan zargin da ake yiwa tsohon kwamandan rundunar IRT, DCP Abba Kyari.
Shugaban kwamitin da Sifeto Janar na yan sanda ya nada don binciken, DIG Joseph Egbunike. ya gabatar da kundin sakamakon binciken ga IGP Mohammed Alkali a ranar Alhamis, 26 ga Agusta, 2021.
Read Also:
Kakakin hukumar yan sanda, CP Frank Mba, ya sanar da hakan a jawabin da ya saki da yammacin nan a shafin hukumar.
A jawabin, DIG Egbunike ya godewa IGP bisa yarda da kwamitinsa da mambobinta da wannan aiki na bincike mai muhimmanci.
Ya bayyana cewa:
“Kwamitin ta fara bincike ba tare da bata lokaci ba kuma wannan kundin rahoton ya kunshi diddigi da gaskiyar abinda ya faru. Hakazalika kundin ya kunshi maganganun Abba Kyari da wasu da ke da alaka da lamarin.”
Bayan gabatar da rahoton, IGP Alkali ya godewa kwamitin bisa aikin da sukayi kuma yayi alkawarin cewa za’a duba rahoton kuma za’a dauki matakin da ya kamata.