Kasar Sin Zata Taimakawa Kasar Najeriya da Magungunan Cutar Korona
Najeriya ta na neman Sin ta taimaka mata da magungunan COVID-19.
Geoffery Onyeama ne ya bayyana haka bayan haduwa da Ministan Sin.
Gwamnatin Tarayya ta yaba da irin gudumuwar da kasar ta bada a da.
Gwamnatin tarayya ta ce ta fara magana da gwamnatin kasar Sin da nufin samun magungunan cutar nan ta COVID-19 ga mutanen Najeriya.
Ministan harkokin kasar wajen Najeriya, Geoffery Onyeama, ya bayyana wannan a lokacin da ya yi magana da manema labarai jiya a garin Abuja.
Hukumar dillacin labarai na kasa, NAN, ta ce Geoffery Onyeama ya zanta da ‘yan jarida ne bayan ya gana da takwaransa na kasar Sin, Wang Yi.
Read Also:
Mista Wang Yi ya kawo ziyarar aiki zuwa Najeriya domin ganin yadda Sin za ta taimakawa kasar.
Ministan harkokin kasar wajen ya bayyana cewa Sin ta taimakawa Najeriya matuka tun da aka fara fama da wannan annoba ta hanyar bada kayan aiki.
Onyeama ya ce a halin yanzu akwai kasashen da su ke kokarin gano maganin cutar, daga ciki har da kasar Sin, kuma Najeriya za ta nemi taimakonta.
“Muna samun gudumuwa sosai daga kasar Sin a bangaren bada kayan aikin likitoci na PPE, sun yi maza sun taimaka mana da kayan.” Inji Onyeama.
Ya ce: “Sin ta na cikin kasashen da ta gano maganin COVID-19, saboda haka muna magana da ita ta taimaka mana da magungunan saboda mutanenmu.”
Daily Trust ta rahoto Ministan yana bayanin niyyar Najeriya na ganin an rika samun jirgin sama wanda zai rika tashi kai tsaye daga Najeriya zuwa Sin.