Harkar Siyasa ta Dukkanin Masu Sha’awar Cigaban ƙasa ne – Gwamna Seyi Mekinde

 

Siyasa a kowane mataki ba na shugabanni da ‘yan siyasar da ke gwamnati bane kawai; ‘yan kasa suna da rawar ganin da za su taka.

Wannan shine ra’ayin Gwamna Seyi Makinde lokacin da yayi magana a cocin Christ Revival Miracle Church a Ibadan a ranar Lahadi, 8 ga watan Agusta.

Gwamnan na Oyo ya ce hanya daya da ‘yan kasa za su samu irin shugabancin da suke so shi ne su shiga siyasa.

Ibadan, Oyo – Ga gwamna Seyi Makinde na jahar Oyo, harkar siyasa ta dukkanin masu sha’awar ci gaban ƙasa da bunkasar ƙas nea.

Wannan shine dalilin da ya sa gwamnan a ranar Lahadi, 8 ga watan Agusta, ya ƙarfafa wa malaman cocin Christ Revival Miracle Church, Ibadan, gwiwar cewa su shiga siyasa.

Gwamna Makinde ya yi wannan kiran ne a lokacin da ya halarci wani taron cocin wanda babban jagoransa, Reverend Peter Folorunso Owa ya shirya.

A cikin jawabinsa, Makinde ya bayyana cewa ta hanyar shiga cikin ayyukan siyasa ne ‘yan ƙasa za su iya samun jerin shugabannin da za su taimaka musu wajen cimma burinsu na gama gari.

Ya ce:

“Na kuma karfafa wa duk wanda ke a nan gwiwar cewa ya shiga siyasa da shugabanci, saboda ta hanyar shigar mu ne jahar mu da kasar mu za su samu irin shugabancin da suke so.”

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here