Ayyukan Sojin Ƙasa ya Bunkasa Harkar Noma a Kudancin Jahar Kebbi – in ji Gwamna Bagudu

 

Gwamnan jahar Kebbi Sanata Abubakar Atiku Bagudu ya bayyana cewa ayyukan rundunar sojin ƙasa a jahar ta samar wa manoma daman zuwa gonakin su ba tare da tsangwama ba, musamman manoman yankin Danko Wassagu wadda tuni suka koma gonakin su.

Sanata Bagudu ya bayyana hakan ne a yayin da Babban hafsan sojojin ƙasa ya kai masa ziyara a gidan gwamnati ranar 19 ga Oktoba 2021 a cikin ziyarar sa a yankin runduna ta 8 ta sojin ƙasan Najeriya.

Gwamnan ya yi kira ga rundunar da su ci gaba da ayyukan su domin samun zaman lafiya a jahar da kuma ƙasa baki ɗaya.

Ya yabawa rundunar domin aikin ta na taimakawa hukumar farar hula.

Ya ƙara da cewa al’umma na goyon bayan masu laifi wadda ya ke jawo rashin tsaro da kuma ta’addanci.

Ya yi kira ga rundunar da ta samar da haɗin kai a tsakanin ta da sauran hukumomin tsaro domin magance ayyukan ƴan fashi daji a yankin arewa maso yamma.

Ya yi alƙawarin baiwa rundunar dukkan goyon baya domin magance matsalar tsaro a jahar

Gwamna Bagudu ya nuna wa babban hafsan sarrafaffun motocin ayyuka domin anfanin rundunar wajen gudanar da ayyukan ta.

Ya yi alƙawarin miƙa motocin da gaggawa domin yin amfani da su wajen ayyukan rundunar.

A jawabin sa, babban hafsan ya yabawa gwamnati da al’ummar jahar Kebbi domin baiwa rundunar haɗin kai wajen gudanar da ayyukan ta.

Ya yi alƙawarin daukar mataki domin yaƙi da ta’addanci da sauran miyagun laifuffuka a jahar.

Ya yi kira ga dukkan masu ruwa da tsaki da su yi dukkan abin da ya dace domin kawo karshen rashin tsaro a yankin.

Babban hafsan ya kai ziyarar ban girma ga Mai Martaba Sarkin Gwandu, Manjo Janar Muhammad Iliyasu Bashar Mai murabus.

Sarkin ya yabawa babban hafsan domin gudanar da ziyarar aiki a yankin rundunar sojojin ƙasan saboda samar da mafita akan matsalar tsaro da ke daƙile ci gaban ƙasan nan.

Babban hafsan ya ziyarci bataliya ta 1 da ke Birnin Kebbi inda ya saurari bayanai akan ayyukan bataliyar a yankin.

Ya kuma yi kira ga dakarun da su zama masu alƙibla da nuna ƙwarewa wajen gudanar da ayyukan su.

Ya tabbatar da cewa za’a samar ma rundunar wadataccen kayan aiki domin gudanar da ayyukan ta.

Birgediya Janar Onyema Nwachukwu

Daraktan Hulda da Jama’a na Rundunar Sojojin Ƙasan Najeriya

19 OKTOBA 2021

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here