Dakarun Sojin Najeriya Sun Kai Farmaki Sansanin ‘Yan ta-da-ƙayar-Baya

 

 

Rundunar sojojin Najeriya ta ce ta kai wani farmaki Juma’a a sansanonin ‘yan Boko Haram a Borno da kuma wasu haramtattun wuraren tace ɗanye mai a jahar Ribas .

Mai magana da yawun rundunar sojin saman ƙasar, Edward Gabkwet ne ya bayana haka cikin wata sanarwa da ya fitar Jumu’a a Abuja.

Gabkwet ya ce farmakin da dakarun sojin ke ci gaba da kai wa a maɓoyar ‘yan ta’addan da masu tayar da ƙayar baya da ɓarayin mai, zai taimaka wajen hana su sakat ta yadda ba za su samu damar haddasa matsala ga tattalin arziki da al’ummar da ba su ji ba ba su gani ba.

Ya ce rundunar Operation Haɗin Kai ta kai farmaki a kusa da ƙauyen Arikna Wojeo bayan samun tabbacin inda maɓoyar ɓata garin ta ke wuraren da suke ci gaba da amfani da su a kudancin Tumbun ku da Tafkin Chadi.

“An bayar da umurnin kai harin, wanda an samu nasara wajen kai shi sakamakon hayaƙi da wutar da aka lura suna tashi da kuma rahotannin da aka samu daga jama’ar yankunan.

Ya ƙara da cewa sahihan bayanan da suka samu sun taimaka wajen fallasa wuraren da ‘yan ta’adda ke amfani da su wajen ɓoye makamai da sauran kayan da suke amfani da su.

“A ranar 13 ga watan Yuni an taɓa kai hari wurin, inda aka samu gagarumar nasara kakkaɓe da dama daga cikinsu, alamu sun nuna cewa ‘yan ta’addan sun sha luguden wuta a wasu yankuna shi ne su ke sake tattaruwa a wannan wuri”, in ji kakakin.

Kakakin rundunar sojin ya kuma ce an ƙara kai wasu hare-hare a yanki Bille da ke ƙaramar hukumar Degema a jahar Ribas, wurin da kakakin ya ce ya yi ƙaurin suna wajen gudanar da haramtattun ayyukan tace mai.

Ya ce an kai farmakin ne da zummar hana tare da karya lagon ɓarayin ta hanyar kawo cikas ga ayyukan da su ke yi, waɗanda ya ce na ci gaba da kawo illa ga muhalli da ma tattalin arzikin ƙasa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com