Sojin Najeriya Sun Kama ƴan Bindiga 10 a Jihohi Biyu
Rundunar Sojin Najeriya ta ce ta bankaɗo gungun masu garkuwa da mutane da kuma aikata laifuka tare da kama mutum 10 da take zargi a jihohin Filato da Taraba na tsakiyar ƙasar.
Wata sanarwa da rundunar ta fitar a yammacin yau Talata ta ce dakarunta na rundunar Operation Whirl Stroke (OPWS) ne suka yi nasarar kama waɗanda ake zargin, inda suka ƙwace bindiga ƙirar AK-47 da kuma ƙunshin harsasai.
Read Also:
Ta ce ta kai samamen ne a jiya Litinin a ƙauyukan Galeri da Kwondo bayan samun bayanan sirri, inda suka kama mutum biyu; Ali Ibrahim da aka fi sani da Yellow, da kuma Wetti Alhaji Ibrahim.
“Mutanen sun amsa laifin yin aiki tare da sanannen jagoran ‘yanfashin daji mai suna Kadogo Fun, wanda ke ayyukansa a yankunan Bangalala da Kampani Zurak na jihar Filato,” in ji sanarwar.
A wani samamen daban, dakarun rundunar sun kama mutum takwas da ke saka kakin soja domin aikata laifuka a kudancin jihar Taraba. “Daga cikin kayayyakin da aka ƙwace daga hannu akwai kakin soja 10, da kuɗi N60,000, da ƙunshin harsasai 30,” in ji sanarwar.