Rundunar Sojin Najeriya ta Kashe Mayaƙan ISWAP 38, ta Daƙile Hari a Borno

Dakarun Sojin Najeriya sun kashe mayaƙan ISWAP guda 38 bayan sun kai hari wani sansanin sojoji a Jihar Borno.

Harin ya faru ne da safiyar ranar Asabar a ƙauyen Mandaragirau da ke Ƙaramar Hukumar Biu.

Dakarun Rundunar Operation Haɗin Kai ne suka mayar da martani tare da daƙile harin.

A wata sanarwa, rundunar sojin ta ce dakarun sun mayar da martani wanda ya tilasta wa mayaƙan tserewa.

Har ila yau, rundunar sojin sama ta taimaka da hare-hare da kuma bayar da bayanan sirri yayin fafatawar.

Bayan harin, sojojin sun bi sahun mayaƙan da suka tsere, inda suka sake kashe wasu.

An gano gawarwaki mayaƙan takwas, yayin da rahotanni suka nuna cewa akwai sama da 30 a wasu hanyoyi da ke yankin.

Sojojin sun kuma ƙwato makamai, ciki har da bindigogi ƙirar AK-47 guda bakwai, alburusai da kuma bama-bamai.

Babu wani soja da ya rasa ransa, amma an lalata wata motar sojoji, yayin da wasu dakarun soji suka jikkata.

Rundunar sojin ta ce har yanzu ana ci gaba da bincike a yankin domin gano ƙarin makamai da gawarwakin mayaƙan da aka kashe, tare da yaba wa sojojin kan jarumtaka da suka yi.

 

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here