Rundunar Sojin Najeriya ta Tarwatsa Sansanin Boko Haram da Kuɓutar da Mutane 30 a Jahar Borno

Rundunar Sojin Najeriya ta bayyana cewa dakarunta na Operation Desert Sanity sun samu nasarar tarwatsa sansanonin ‘yan ƙungiyar ISWAP da Boko Haram a ƙauyukan Ndufu da Musuri da ke jihar Borno.

Rundunar ta ce ta kuɓutar da mutum 30 wadanda aka yi garkuwa da su.

Har wa yau, sanarwar ta ƙara da cewa dakarun soja sun ƙwato makamai daga hannun ‘yan bindigar masu iƙirarin jihadi.

Jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya ta shafe shekaru fiye da 10 tana fama da hare-haren ‘yan Boko Haram masu ikirarin jihadi wanda ya yi sanadiyyar salwantar rayukan mutum fiye da 300,000, a cewar Majalisar Ɗinkin Duniya.

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here