Dakarun Sojin K’asa Sun Hallaka Gawurtaccen ‘Dan Awaren IPOB/ESN Ejike da ‘Yan Bindiga Uku a Jihar Anambra
Dakarun rundunar sojin k’asan Najeriya da ke yankin Kudu maso Gabas sun samu nasarar hallaka gawurtattun y’an k’ungiyar aware ta IPOB/ESN hud’u a garin Ihiala da ke jihar Anambra. Tsagerun Wad’anda sun fito ne domin tilastawa al’ummar yankin zaman gida da farko, sun bud’e wuta ne kusa da gidan mai da ke garin Ihiala. Dakarun mu bayan samun bayanai ta kiran waya, sun mamaye yankin, inda suka bud’e wuta da fafatawa mai tsawo. Dakarun sun samu nasarar hallaka jagoran y’an awaren mai suna Ejike da sauran tsagerun uku.
Read Also:
Dakarun namu kuma sun k’wato Babur d’aya, da bindigogi biyu k’irar harbi ka ruga, harsasai 12 da tabar wiwi da kuma sauran kayayyaki da dama.
Haka kuma, an sami tsautsayi, inda motar dake d’auke dakarun mu ta samu had’ari inda muka rasa hafsa d’aya da soja d’aya. Sa’an nan sojojin mu biyu sun sami raunuka kuma suna samun kulawa a asbitin mu a yankin.
Bayan nuna matuk’ar juyayin mu na rashin jajirtattun dakarun mu, muna kuma kira ga al’umma da kuma sauran hukumomin tsaro da su bamu had’in kai ta han’yar samar da muhimman bayanai da zai taimaka wajen tabbatar da zaman lafiya a yankin.
Birgediya Janar Onyema Nwachukwu
Daraktan Hulda da Jama’a na Rundunar Sojin Kasan Najeriya
9 FABARAIRU 2022