Rundunar Sojin Najeriya ta Kashe Mayakan Boko Haram 49 a Jihar Borno

 

Rundunar sojin Najeriya ta bayyana kashe mayakan Boko Haram 49 a wasu hare-hare ta sama da jiragen yaki na Super Tukano suka yi kan ‘yan ta’addar a jihar Borno.

An ruwaito cewa rundunar Operation Hadin Kai ne suka kai hare-haren ta sama a ranakun 30 da kuma 31 ga watan Agusta a sansanoninsu a Gargash da Minna da Gazuwa da ke cikin karamar hukumar Bama na jihar ta Borno.

A cewar wani masani kan tsaro da dakile hare-haren ta’addanci, Zagazola Makama a tafkin Chadi, ya ce hare-haren ta sama na ranar 30 ga watan Agusta, sun kuma fada kan wata babbar motar ‘yan tada kayar bayan da ke tafiya tare da kashe daukacin wadanda ke cikin motar.

A ranar 31 ga watan Agusta, an samu bayanan sirri da suka nuna mayakan na hada-hadar aikin kudi, inda nan take aka kai musu hari da kashe wasu daga ciki.

Shaidu sun ce an akshe akalla ‘yan ta’adda 29 a Gazuwa da kashe wasu da ke tafiya cikin mota guda hudu a Gargash, yayin da mayaka 16 kuma suka gamu da ajalinsu a garin Minna.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here