Rundunar Sojojin Najeriya Sun Kama Mota Dauke da Tulin Miyagun Makamai

 

Rundunar sojojin Najeriya sun ce sun ci karo da wata mota da ta kinkimo tulin miyagun makamai.

Motar ta biyo ta gaban Dakarun Sojoji don haka aka nemi a tsaida direban, amma ya ki tsayawa.

Nan take aka budawa motar wuta, da aka bincika sai ga ta ta dauko bama-bamai, harsahi da khaki.

Cross River – Rundunar sojojin Najeriya sun bada sanarwar kama wata mota da ta dauko makamai. Wannan lamarin ya faru ne a jihar Kuros Riba.

A wata sanarwa da ta fito a ranar Laraba, 22 ga watan Yuni 2022, an fahimci sojojin 13 Brigade da ke karkashin dakarun 82 Div ne suka yi wannan kokarin.

Jaridar Vanguard ta ce jami’an tsaron kasar sun samu makaman ne a wata mota kirar Toyota Camry mai lambar garin Jalingo a jihar Taraba (JAL 492 AA.)

Motar ta na kokarin wucewa zuwa kauyen Utanga daga yankin tsaunukan Obudu a Kuros Riba.

Sanarwar da ya fito daga Hedikwatar sojojin kasa ya tabbatar da cewa sojoji sun yi kokarin tare wannan mota, amma sai direban ya ki tsayawa, ya zura a guje.

Sanarwar da aka fitar “Taurin kan direban ya tursasawa sojojin suka budewa tayoyin motar wuta, suka hana ta tafiya.”

“Da aka yi bincike da kyau, an gano cewa motar ta na dauke da kayan bam-bamai na IED 72, ruwan bam 121, casbi 200 na harsahin NATO mai mita 7.62.”

Haka zalika an kuma samu zagaye 82 na casbin wani harsashi na musamman mai tsawon mita 7.62 “Sauran kayan da aka samu a motar sun hada da khaki da kuma kayan sojoji.”

– Hedikwatar Sojoji Jaridar ta ke cewa sanarwar ta yi kira ga jama’a su ba jami’an sojoji hadin-kan da ake bukata ta hanyar taimaka masu da bayanan da za su taimakawa aikinsu.

Idan sojoji su na samun irin wadannan bayanai, za a magance matsalar tsaro a fadin kasar nan.

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here