Sojojin Najeriya Sunyi Artabu da Mayakan Boko Haram a Yobe
Sojojin Najeriya sun fafata da wasu da ake zargin mayakan Boko Haram ne a Babbangida dake jahar Yobe.
Mazauna garin Babbangida, Hedkwatar karamar hukumar Tarmuwa, sun tsorata da harin, inda suka tsere cikin jeji.
Rahotanni sun nuna cewa wani soja ɗaya ya samu raunuka a fatatawar, kuma ana cigaba da bashi kulawa.
Yobe – Dakarun sojoji na rundunar sojojin Najeriya sun fatattaki gungun mayakan Boko Haram ranar Laraba a jahar Yobe.
Wata majiya mai karfi daga cikin rundunar ta shaidawa Channels tv cewa sojojin sun samu nasarar kwato motar Toyota ɗaya daga cikin uku da mayakan suka zo da su.
Sai dai soja ɗaya ya samu rauni inda yake cigaba da amsar kulawar lafiya bayan harin yan ta’addan.
Read Also:
An yi wannan artabu ne yayin da yan Boko Haram suka yi kokarin kutsawa garin Babbangida, hedkwatar karamar hukumar Tarmuwa a jahar Yobe.
Mazauna garin sun tsorata
Wani mazaunin garin Babbangida, Audu Yakubu, yace maharan sun zo a motocin ɗaukar kaya Toyota guda uku, inda suka tunkari sansanin sojoji kai tsaye.
Yakubu yace:
“Wasu yan kauye sun ankarar da mu cewa sun ga bakin fuska a kan hanyar Babbangida, saboda haka muna ganin isowarsu muka tsere cikin jeji don tsira da rayuwarmu.”
Wani mazaunin yankin da ya nemi a ɓoye sunansa yace maharan sun farmaki garin ne da misalin karfe 6:15 na yamma, inda suka buɗe wuta kan mai uwa da wabi.
Sai dai a bayaninsa yace dakarun sojoji sun kawo ɗauki cikin gaggawa inda suka maida martani, a ka yi musayar wuta tsakaninsu.
Babbangida yana da nisan kilomita 50 daga garin Dapchi, inda a baya wasu mahara suka sace ɗalibai mata 110 daga makarantar sakandiren mata a watan Farairun shekarar 2018.