Sojojin Najeriya Sun Ceto Mutane 101 Daga Hannun ƴan fashin Daji a Jihohi Biyu 

 

Sojojin Najeriya ƙarƙashin rundunar Operation Fansan Yamma sun ce sun ceto mutum 101 da aka yi garkuwa da su a ƙananan hukumomin Ƙanƙara da ke jihar Katsina da kuma Shinkafi a jihar Zamfara.

Shugaban sashen yaɗa labarai na rundunar, Laftanar-kanar Abubakar Abdullahi ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Laraba.

Sanarwar ta ce rundunar ta samu nasarar ce a wani samame da ta ƙaddamar kan dabobin ƴan fashin daji a ranakun 17 da 18 ga wannan wata na Maris.

Sanarwar ta ƙara da cewa a lokacin samamen an kashe ƴan fashi 10 a fafatawar da aka yi tsakanin dakaru da ƴan fashin a yankin Faru na ƙaramar hukumar Maradun.

Haka nan sanarwar ta ce an fara samamen ne daga yankin Tudun Pauwa na ƙaramar hukumar Ƙanƙara a jihar Katsina, inda aka kashe ƴan fashin daji uku tare da ceto mutum 83 da aka yi garkuwa da su.

Sannan bayan tattara bayanan sirri, rundunar ta kai farmaki a Bagabuzu na yankin Faru a jihar Zamfara, inda ta kashe ƴan fashi 7 da ƙwato wasu kayayyaki, ciki har da babur.

Zamfara da Katsina, jihohi ne da ke fama da matsalar ayyukan ƴan fashin daji wadanda ke kai farmaki a ƙauyuka, suna kisa da kuma garkuwa da mutane domin neman kudin fansa.

Dukkanin jihohin biyu sun kafa rundunonin sintiri wadanda ke taimaka wa dakarun sojin Najeriya wajen yaƙi da matsalar, wadda aka shafe shekara da shekaru ana fama da ita.

Hare-haren ƴan bindigan sun haifar da asarar rayuka da durƙusar da ayyukan tattalin arziƙi a yankunan, tare da tarwatsa mutane daga muhallansu.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here