Sojoji Sun Ceto Mutane 3 Daga Hannnun ‘Yan Ta’adda a Jihar Borno

 

Majiyoyin sun ce sojojin sun kai samame kan ’yan ta’addan kuma sun yi nasarar ceto dukkan waɗanda abin ya shafa su uku a lokacin aikin.

Sojojin Operation Haɗin Kai sun ceto fararen hula uku da aka sace tare da ƙwato harsasai a lokacin wani samame akan ’yan ta’adda a ƙaramar hukumar Bama da ke jihar Borno.

Majiyoyin tsaro sun ce an gudanar da aikin sintirin ne da misalin ƙarfe 10:00 na safe a ranar 30 ga Maris, a ƙarƙashin sojojin Bataliya ta 202 tare da haɗin gwiwar sojojin sa kai na BOCOBS.

A cewar majiyoyin, sojojin sun mayar da martani ga bayanan sirri masu inganci da ke nuna cewa waɗanda ake zargin ‘yan ƙungiyar ISWAP ne da kuma Boko Haram suka sace mutane uku a yankin.

Majiyoyin sun ce sojojin sun kai samame kan ’yan ta’addan kuma sun yi nasarar ceto dukkan waɗanda abin ya shafa su uku a lokacin aikin.

Abubuwan da aka gano daga wurin waɗannan ’yan ta’addan sun haɗa da wata bindiga ƙirar AK-47 guda ɗaya ɗauke da harsasai 30 na musamman nau’in 7.62mm.

Majiyoyin sun ƙara da cewa, waɗanda aka ceto suna cikin ƙoshin lafiya, yayin da sojoji suka ci gaba da mamaye yankin gaba ɗaya don hana sake afkuwar lamarin.

Sun ce, aikin wani ɓangare ne na ci gaba da ƙoƙarin kare fararen hula da kuma wargaza ayyukan ta’addanci a faɗin yankin Arewa maso Gabas.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here