Mamaye Garin Kala-Balge: Sojojin Najeriya Sun Dakile Harin ‘Yan Ta’addan Boko Haram a Jahar Borno

 

‘Yan ta’addan Boko Haram sun kai hari garin Rann, hedkwatar garin Kala-Balge a jahar Borno.

Sojojin Najeriya sun samu nasarar dakile harin, sun kuma hana ‘yan ta’addan shiga garin na Rann.

Wasu mutane biyar sun ji raunuka, yayin da wata mata ta rasa ranta a asibiti sakamakon harbin bindiga.

Akalla mutum daya farar hula ya rasa ransa yayin da wasu biyar suka jikkata lokacin da wasu da ake zargin ‘yan kungiyar Boko Haram ne suka yi yunkurin kutsawa cikin garin Rann, hedkwatar karamar hukumar Kala-Balge da ke jahar Borno, in ji majiyar tsaro.

Lamarin ya faru ne lokacin da haramtacciyar kungiyar ta mamaye garin Rann da misalin karfe 6:15 na maraice suna harbe-harbe amma suka gamu da turjiya daga sojojin Najeriya.

Wata majiyar tsaro ta tabbatar da cewa sojoji sun yi amfani da bindigoginsu a yayin harin da aka kai lamarin da ya haifar da sakamakon lalata motar bindigogi ta maharan, Daily Trust ta ruwaito.

ajiyar ta ce mutane biyar, ciki har da ‘yan kungiyar hadin gwiwa ta farin kaya (JTF) sun samu rauni a harin.

“Wata farar hula (wata baiwar Allah) daga baya ta mutu sakamakon harbin bindiga da ya same ta a cinyarta.

A yayin harin, mutane biyar sun ji rauni sakamakon harbi da bindiga kuma yanzu haka suna ci gaba da karbar magani a sansanin sojoji.

”Sojoji ba su bar maharan sun shigo garin ba, sun fara fatattakarsu a bakin kofa. Wannan gagarumin aiki ne ga sojoji a Rann.” Inji majiyar.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here