Rundunar Sojoji ta Fadin Dalilin Soke Taron da Zatai
Babban jami’in rundunar sojan Najeriya da ke hallartar taron shekara-shekara ta babban hafsan sojan kasar Najeriya ya kamu da korona.
Hakan ya tilasatawa rundunar soke sauran abubuwan da aka shirya gudanawar yayin taron a birnin tarayya Abuja.
An bukaci sauran jami’an soja da suka hallarci taron su killace kansu na kwanaki 14 nan take.
An soke sauran shirye shiryen da za a gudanar a wurin taron shekara shekara na babban hafsan sojan kasar Najeriya da ke gudana a Abuja.
Nigerian Tribune ta ruwaito cewa an dauki wannan matakin ne bayan wani babban jami’in soja da ke halartar taron ya kamu da korona a Abuja.
Read Also:
Direktan sashin hulda da jama’a na rundunar soji, Birgediya Janar Sagir Musa ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa ta ya raba wa manema labarai.
Bisa tsarin gwamnatin tarayya na cutar Covid 19, an bukaci dukkan mahalarta taron da su killace kansu ba tare da bata lokaci ba don kiyaye yaduwar kwayar cutar.
Wani bangare na sanarwar ya ce, “saboda sake hauhawar masu dauke da kwayar cutar covid 19 a Abuja a wani abu mai kama da zagaye na biyu na annobar da kuma abu mara dadi da ya faru a ranar 8 ga watan Disamban 2020 inda wani jami’i da ke hallartar taron shekara-shakara na babban hafsan sojan kasar Najeriya na 2020 a Abuja, an soke taron.
“An kuma bukaci dukkan mahalarta su killace kansu.”
Kazalika, The Nation ta ruwaito cewa an rage adadin bakin da aka gayyata daurin auren Hamisu Tukur Buratai, dan babban hafsan sojojin kasa na Najeriya, Tukur Buratai.