Sojoji Sun Kai wa Ofishin Jakadancin mu Hari a Sudan – Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa

 

Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ta ce an kai hari kan gidan jakadanta da ke Khartoum da jiragen sojin Sudan.

A wata sanarwa da ta fitar a shafin sada zumunta, ma’aikatar harkokin ƙetare na cewa za ta shigar da ƙorafinta a duk wuraren da ya kamata ciki har da Majalisar Ɗinkin Duniya.

A baya an sha zargin Daular da taimaka wa dakarun RSF da makaman da suke amfani da su wajen yaƙi da sojojin Sudan a kazamin yaƙin da ake gwabzawa a kasar. Sai dai ƙasar ta sha musanta wannan zargi.

A jiya Lahadi, mayaƙan RSF, sun fito suna cewa babu batun sulhu da sojoji domin kawo ƙarshen yaƙin watanni 17

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here