Rundunar Sojojin Najeriya ta Kama ‘Yan Ta’addan Boko Haram 10 a Jahar Kano

Rundunar sojojin Najeriya ta tabbatar da kamun wasu mutane da ake zargin yan ta’addan Boko Haram ne a jahar Kano.

Mai magana da yawun runduna ta 3 ta sojojin Najeriya da ke Kano, Kyaftin Njoko Irabor ne ya tabbatar da hakan.

Sun shiga hannu ne lokacin da sojojin suka kai mamaya Filin Lazio da ke Unguwar Hotoro a cikin garin Kano a ranar Asabar da yamma.

A ranar Lahadi, 9 a watan Mayu ne rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da samamen da ta kai ga kame wasu da ake zargin ‘yan kungiyar Boko Haram ne a jahar Kano.

Mai magana da yawun runduna ta 3 ta sojojin Najeriya da ke Kano, Kyaftin Njoko Irabor ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai amma bai bayar da takamaiman adadin wadanda aka kama ba.

Kodayake, majiyoyi a yankin sun sanya adadin wadanda ake zargin zuwa 10, jaridar Vanguard ta ruwaito.

An tattaro cewa an kama wadanda ake zargin ‘yan ta’addan ne lokacin da sojojin suka kai mamaya Filin Lazio da ke Unguwar Hotoro a cikin garin Kano a ranar Asabar da yamma don mamaye masallaci da wasu gidaje da ake zargin na wasu ‘yan jahar Borno ne da suka tsere daga yankin arewa maso gabas da ke fama da rikicin Boko Haram.

Kyaftin Irabor ya ce, “Ee, an gudanar da aikin a yankin kuma zai kasance shiri da za a ci gaba da aiwatarwa”.

A daidai lokacin, Kakakin rundunar ya yi alkawarin ba da cikakken bayani kan aikin da kuma yawan wadanda aka kama yayin aikin wanda ya dauki sama da awa guda.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here