Mutane 15 Sun Rasa Rayukansu Sanadiyyar Kifewar Jirgin Ruwa a Jahar Neja

 

Kifewar wani jirgin ruwa ya yi sanadiyyar mutuwar mutane akalla 15, yayin da wasu suka nutse a wani yankin jahar Neja.

An ruwaito cewa, lamarin ya fuwa ne da yammacin ranar Asabar lokacin da mutanen suka dawo daga kasuwa.

Rahoto ya bayyana cewa, jirgin na dauke da mutane sama 60, ciki har da mata da yara kanana Iftila’in ya faru ne a karshen mako a jahar Neja, biyo bayan hatsarin jirgin ruwan da ya faru a garin Tijana na karamar hukumar Munya da ke jahar wanda ya kai ga mutuwar mazauna kauye sama da 15 a cikin jirgin ruwan a cikin wani kogi da ke yankin.

Jirgin ruwan ya kife ne da misalin karfe 6:00 na yamma a ranar Asabar lokacin da ake zargin mazauna kauyen sun dawo daga wata kasuwar yankin da ke Zumba a karamar hukumar Shiroro ta jahar.

A cewar Sarkin Kasuwar na Zumba, Malam Adamu Ahmed wanda ya tabbatar da afkuwar lamarin ga Tribune Online, ya ce jirgin na dauke da akalla fasinjoji 60, ciki har da mata da yara lokacin da ya kife saboda wata guguwar iska mai karfin gaske.

Ya ce daga cikin wadanda lamarin ya rutsa da su akwai wasu wadanda suka dawo gida da a baya suka gudu daga gidajensu tare da yaransu saboda hare-haren ‘yan bindiga.

Ya ci gaba da cewa kimanin mutane 17 aka ceto da rai a kokarin wasu amzauna yankin wadanda suka fara kai dauki jim kadan bayan faruwar lamarin biyo bayan kiran neman agaji da wasu da abin ya shafa suka yi a kusa da inda jirgin ya kife.

Sarkin kasuwa ya kuma bayyana yadda matasa suka yi namijin kokari wajen ganin sun ceto mutane daga halaka, tare da kokawa cewa, har yanzu ba a samu wani taimakon gwamnati ba.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here