Buhari Bai da Karfin Tunani da Lafiyar Jagorantar Najeriya: Gwamnatin Kaduna ta Musanta Batun da Aka Alakanta Gwamna El-Rufai da Shi

 

Gwamnatin jahar Kaduna ta karyata wani wallafar jaridar yanar gizo da aka alakanta da gwamnanta kan Shugaba Muhammadu Buhari.

Gwamnatin ta Kaduna ta ce El-rufai bai taba cewa Buhari bai da karfin tunani da lafiyar jagorantar Najeriya ba.

Ta bayyana hakan a matsayin makircin wasu mutane don haifar da rudani a siyasar kasar.

Gwamnatin jahar Kaduna ta ce Nasir El-Rufai, gwamnanta, bai bayyana Buhari a matsayin wanda ba shi da karfin tunani da lafiyar iya jagorantar Najeriya ba.

Wannan magana an danganta ta ne ga gwamnan a wani rahoto da wani dandalin yanar gizo ya wallafa.

A wata sanarwa a ranar Asabar, Samuel Aruwan, kwamishanan tsaron cikin gida na Kaduna, ya ce ikirarin karya ne.

Ya ce wadanda ke da alhakin wallafar suna neman haifar da “tashin hankali da rudani me a cikin siyasar kasar”, jaridar The Cable ta ruwaito.

Aruwan ya bukaci jama’a da su yi watsi da dandalin da ke “kokarin wucewa a matsayin shahararriyar jaridar yanar gizo don yada makircinsu”.

Sanarwar ta ce: “An wallafa wani rahoton bogi a yanar gizo a kan Shugaba Muhammad Buhari inda suka danganta shi ga Gwamna Nasir El-Rufai.

“Manufar tawagar da ke da alhakin yada labarin karyar da makircin shine, saboda haifar da rikici da rudani a cikin siyasar kasar.

“Dukkanin labaran an kirkiresu ne, kuma suna kokarin wucewa a matsayin shahararriyar jaridar yanar gizo don yada makircinsu.

“Gwamnatin Jahar Kaduna ta bukaci jama’a da su yi watsi da wannan wallafar kuma su dauke shi a matsayin karya ce kawai.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here