Sojojin Najeriya Sun Kama Masu Kai wa ‘Yan Bindiga Makamai

 

Sojojin Najeriya tare da takwarorinsu na tsaro sun kama wasu mutane 15 da ake zargi da samar wa ‘yan bindiga makamai da sauran kayan aiki.

Cikin wata sanarwa da sojojin suka wallafa a shafinsu na X, inda suka ce an yi kamen ne bayan samun bayanan sirri kan mutane.

Sanarwar ta ƙara da cewa an kashe wani mutum guda da ake zargin ɗan bindiga ne yayin wannan samamen a wurare da dama.

A yayin saman dakarun Najeriya sun yi nasarar kama makamai masu dama da harsasai da kuma wasu kayayyaki na daban.

“A ranar 30 ga watan Agusta 2024, dakaru sun kai hari kan ‘yan bindiga da masu yi musu jigilar kayayyakinsu a Mararaba Donga da ƙauyen Manya da suke a Ƙananan hukumomin DDonga da Takum a jihar Taraba.

“An kama mutum biyar da ake zargi a lokacin samamen, an kuma kamaya kayayyaki kamar haka: bindiga uku ƙirar AK-47, bindiga biyu ƙirar cikin gida, bindiga biyu ƙirar da ba ta gida ba, bindiga biyu ta farauta, wata bindiga mai ɗaukar harsashi 61 da dai sauransu.

“A Yobe dakarun sun kama wasu masu kaiwa mayaƙan Boko Haram kayan aiki a ƙauyen Jimbal da ke ƙaramar Hukumar Tarmuwa.

“A Kaduna an kama makamantan waɗannan mutane masu kai kayan aiki a ƙauyen Rijana a ƙaramar Hukumar Chikun. Tare da su akwai wayoyi uku da ke da katin waya sama da naira 100,000, an kuma samun garin kuɗi naira 1,532,900.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here