Rundunar Sojoji ta yi Nasarar Kashe Wasu ‘Yan Fashi

Rundunar sojin Operation Safe Heaven ta kashe ‘yan fashi da makami 3 a garin Filato.

An halaka su ne a ranar Laraba yayin da suke sintiri a sansanin bautar kasa da ke Mangu.

An kama ‘yan fashin ne yayin da suka tarkato wasu kayayyaki da suka hada da wayoyi.

Sojojin atisaye na musamman (Operation Safe Heaven), masu wanzar da zaman lafiya sun kashe ƴan fashi uku, kamar yadda kwamandansu, Chukwuemeka Okonkwo, ya faɗi kuma Premium Times ta rawaito.

Mr Okonkwo ya bayyana hakan ne ga kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) a ranar Alhamis a garin Jos.

Ya ce uku daga cikin ƴan fashin sun tsere da raunukan alburushi.

“A daren ranar Laraba ne mazajen mu suka sheƙe ƴan fashi a titin sansanin ƴan bautar ƙasa (NYSC) da ke Mangu.”

“Ƴan fashin sun sace kayayyakin da suka haɗa da wayoyi da sauran muhimman abubuwa.”

“Bayan sojojin mu sun ɗauki lokaci suna tirzawa da su, an yi nasarar sheƙe uku daga cikin su shida.”

“Sauran kuma sun tsere da raunukan harsashi zuwa maƙwabtan ƙauyuka,” a cewarsa.

Kwamandan ya ce an ƙwato wasu makamai daga hannunsu wanda suka haɗar da bindigun gargajiya biyu, ƙananun bindigu 5, da sinƙin fakitin alburusai.

Ya ce an miƙa gawarwakin matattun ‘yan ta’addadar zuwa Caji Ofis ɗin ƴan sanda dake Mangu.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here