Yadda Sojojin Sama da na Kasa Suka Kashe ‘Yan Bindiga 70 a Jahar Neja

 

Ayyukan sojojin sama da na kasa na Operation Gama Aiki (OPGA) suna cigaba da haifar da sakamako mai kyau.

An samu bayanai akan yadda mazauna yankin jahar Neja suka bayyana yadda aka kashe ‘yan bindiga 70.

A ranar 5 ga watan Augustan 2021 ne ‘yan bindigan suka sha wannan ragargazar a yankin Jasuwan Garba-Urege.

Niger – Ayyukan hadakar sojojin sama dana kasa na Operation Gama Aiki (OPGA) suna kara samar da nasarori na ban mamaki.

PR Nigeria suna cigaba da tattaro bayanai akan yadda ‘yan bindigan dake da sansani a yankin Jasuwan Garba-Urege a jahar Neja sun sha ragargaza a wurin sojojin sama na OPGA da suka yi amfani da Agusta 109 da EC 135 jiragen yaki.

Yadda ragargazar ta kasance Wani babban jami’in tsaro wanda har da shi aka yi ragargazar ya ce sai da jirgin saman ya bi a sannu wurin gano asalin wuraren da miyagun mutanen suka yi dandazo sannan ya harba abubuwa masu fashewa a wuraren.

An hango yadda sansanonin nasu suka yi ta kamawa da wuta sakamakon harbin da suka sha’

Rahotonni daga mazauna yankin sun tabbatar da yadda ‘yan bindiga 70 suka bakunci lahira. Anyi wannan ragargazar ne a ranar 5 ga watan Augustan 2021.

Kuma makamancin haka ya kara aukuwa a ranar 6 ga watan Augustan 2021 wanda sojojin sama suka yi a Kwawu da Uzawo dake jahar Neja inda aka ragargaji ‘yan ta’adda da dama.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here