Sojojin Najeriya Sun Kashe ƴan Ta’addan Boko Haram a Borno
Dakarun sojojin Najeriya sun yi abin a zo a gani bayan sun sheƙe ƴan ta’addan Boko Haram a wani samame a jihar Borno a Arewa maso Gabas.
Sojojin na bataliya ta 151 da ke aiki a rundunar Operation Hadin Kai sun hallaka ƴan ta’adda takwas yankin Bula Marwa da ke jihar.
A wata sanarwa da rundunar ta fitar, ta ƙara da cewa sojojin sun yi nasarar ƙwato makamai tare da wasu kayayyaki daga hannun ƴan ta’addan.
Read Also:
Sanarwar ta ce ƴan ta’addan sun gamu da ajalinsu ne a ranar 28 ga watan Yulin 2024 a yayin wani samame da sojojin suka kai a maɓoyarsu, rahoton tashar Channels tv ya tabbatar.
Dakarun sojojin sun kuma ƙwato abin harba gurneti, bindiga ƙirar MK da wata jaka mai ɗauke da kayan ƴan ta’addan. Sanarwar ta ƙara da cewa dakarun sojojin na ci gaba da bincike a yankin domin zaƙulo ragowar ƴan ta’addan da ke wajen.
Rundunar sojojin ta bayar da tabbacin cewa jami’anta za su ci gaba da haɗa kai da sauran hukumomin tsaro domin ci gaba da kare lafiya da dukiyoyin jama’a da kawo ƙarshen ayyukan ta’addanci.