Ta’addanci da Garkuwa da Mutane: Rundunar Sojoji ta Tura Dakarun Sojoji Mata 300 Hanyar Abuja-Kaduna
Rundunar sojoji ta tura rundunar dakarunta mata zalla 300 zuwa babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna.
Gwamnan jahar Kaduna, Nasir El-Rufa’i, ya jagoranci tawagar jami’an gwamnatinsa domin tarbar rundunar sojojin.
El-Rufa’i ya bayyana cewa ganin rundunar matan ya kara masa karfin gwuiwar cewa nan bada dadewa ba batun garkuwa da mutane da sauran aiyukan ta’addanci a hanyar zai kare.
Read Also:
Rundunatr sojin Nigeria ta jibge dakarunta mata guda 300 a babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna domin su bayar da gudunmawa wajen yakar ‘yan ta’addar da suka addabi hanyar.
A ranar Laraba ne rundunar soji ta sanar hakan tare da bayyana cewa dakarun mata zasu karawa takwarorinsu maza karfi a kokarinsu na ganin bayan ‘yan bindiga a babbar yanyar da kewaye.
Gwamnan jahar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa’i, ne ya tarbi rukunin farko na dakarun sojin bayan isowarsu Kaduna.
El-Rufa’i ya jagoranci tawagar gwamnatinsa da suka hada da mataimakiyarsa, Hadiza Balarabe, zuwa bakin babbar hanyar da ta shigo garin Kaduna domin yi wa ayarin sojojin maraba.
Yayin da yake gabatar da jawabin yi musu marhabun, El-Rufa’ ya bayyana cewa zuwan dakarun ya kara masa karfin gwuiwar cewa nan bada dadewa ba batun ‘yan bindigar da suka addabi babbar hanyar zai zama tarihi.