Rundunar Sojojin Kasa ta Najeriya ta Musanta Rahotan Dake Cewa ‘Yan Ta’adda ke Rike da Garin Damasak
Rundunar sojin kasa ta Najeriya ta musanta labarin dake cewa ‘yan ta’adda sun kwace garin Damasak.
Kamar yadda kakakin rundunar ya sanar, tabbas ‘yan ta’adda sun kai hari amma sojoji ke rike da garin a halin yanzu.
Ya ce Birgediya Janar S.S Tilawan ya yawata garin da rana kuma ana cigaba da kokarin kakkabo ragowar ‘yan ta’addan Rundunar sojin kasa ta Najeriya ta ce rundunarta ta Operation Lafiya Dole ce ke rike da garin Damasak dake karamar hukumar Mobbar ta jahar Borno.
A ranar Talata ne aka tabbatar da cewa ‘yan ta’addan Boko Haran sun kai farmaki garin.
Read Also:
Daraktan hulda da jama’a na rundunar, Birgediya Janar Mohammed Yerima, ya bayyana hakan a wata takarda da ya fitar a ranar Alhamis a garin Abuja.
Yerima ya ce rahotannin da wasu bangare na kafafen yada labarai ke bayyana na cewa ‘yan ta’adda sunkwace garin Damasak duk babu gaskiya a ciki.
Ya ce tabbas ‘yan ta’addan sun kai farmaki garin amma kuma cike da kwarewa zakakuran sojin suka fatattake su.
“A halin yanzu da muke magana, dakarun ne ke rike da yankin. Kwamandan birged ta biyar, Birgediya Janar S.S Tilawan na yawo a garin domin duba yadda garin yake bayan harin ‘yan ta’adda,” yace.
Daraktan yace ‘yan ta’addan sun shiga garin ta yankin arewaci tare da hadin bakin wasu mazauna yankin.
“Rundunar sojin kasa na tabbatar wa da mazauna Damasak da yankunan kusa da su kwantar da hankalinsu domin ana cigaba da kakkabo ragowar ‘yan ta’addan dake wasu sassan garin,” yace.