Rundunar Sojojin Kasa da na Sama Sun Ragargaji ‘Yan Boko Haram-ISWAP a Jahar Borno

Hadakar rundunonin sojojin kasa da na sama sun ragargaji ‘yan Boko Haram da dama dake yankin Gubio a jahar Borno.

Kamar yadda wani jami’in binciken sirri ya tabbatar, sojojin saman sun yi ta harbi ta sama suka kone miyagun makamai ‘yan ta’addan.

Bayan jin aman wuta ta sama, ‘yan ISWAP din sun fara tserewa take a nan sojojin kasa suka bude musu wuta suka karkashe su.

Gubio, Borno – Hadakar rundunonin sojojin kasa da na sama sun ragargaji ‘yan ta’addan Boko Haram-ISWAP a wuraren Gubio dake jahar Borno.

Wani jami’in binciken sirri ya sanar da PRNigeria cewa a kalla motocin yaki hudu sojojin sama dana kasa suka lalata yayin ragargazar ‘yan ta’addan.

Dalla-dalla: Yaya al’amarin ya faru?

Lamarin daya faru ne a ranar Litinin ya yi sanadiyyar mutuwar ‘yan ta’addan da dama.

PRNigeria ta fahimci yadda rundunar sojojin kasa suka fuskanci ‘yan ta’addan yayin da jirgin sojojin NAF kuma ya fita wani aikin na daban aka umarce shi da ya cigaba da aiki a wuraren Gubio.

Bayan jirgin NAF ya hango ‘yan Boko Haram suna yawo da motocin yakinsu guda hudu take anan suka fara auna musu harbi ta sama daga nan suka dakatar dasu.

Bayan harbe-harben, wasu daga cikin ‘yan ta’addan sun so su tsere amma take a nan sojojin kasa suka kashesu.

Baya ga lalata motocin yakinsu, an samu miyagun makamai daga hannunsu kamar bindigogi masu jigida, harsasai, jarkoki, tabar wiwi, magungunan inganta jima’i, littattafai wadanda akwai hanyoyin hada bama-bamai da sauransu,” a cewarsa.

Ina ‘yan ta’adda suka nufa bayan jin ruwan wuta?

Bayan wadannan rahotonnin an samu labarin yadda ‘yan ta’addan suka fara tafiya tsakanin Sambisa zuwa Parisu zuwa yankin Njimiya yayin da wani jirgin saman yayi gaggawar ragargazar ‘yan Boko Haram din.

Yayin da aka tambayi kakakin NAF, Air Commodore Edward Gabkwet ya sanar da PRNigeria cewa harin da suka kai ya haifi da mai ido.

Ba zan iya bayar da bayanai akan lamarin da ya faru a ranar Litinin ba, sojojin sama sun samu nasarar lalata motocin yakinsu yayin da sojojin kasan suka ragargaji ‘yan ta’addan da suke kokarin tserewa.

Kwamandan sojin, Janar Christipher Musa ya yabawa rundunar sojojin akan kokarin da sojojin kasa dana sama suka yi na ragargazar ‘yan ISWAP-Boko Haram din a maboyarsu.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here