Sojoji Sun Ragargaji ‘Yan Ta’addan ISWAP da ‘Yan Fashin Daji a Jahar Sokoto

 

Sojojin rundunar Operation Hadarin Daji tare da wasu cibiyoyin tsaron sun ragargaji ‘yan ta’addan ISWAP da ‘yan fashin daji.

Miyagun sun kai farmaki sansanin sojojin ne yayin da wasu sojojin suka tafi inda aka tura su ayyukan tsaron jama’a.

Tuni kuwa dakarun suka ragargaji ‘yan bindigan tare da bin wasu har kauyen Bassira da ke jamhuriya Nijar

Sokoto- Dakarun rundunar Operation Hadarin Daji, tare da hadin guiwar sauran hukumomin tsaro sun halaka miyagun ‘yan ta’addan Islamic States for West African Province, ISWAP da ‘yan bindiga a jahar Sokoto.

Wannan na kunshe ne a wata takarda da daraktan yada labaran tsaro, Manjo Janar Benjamin Sawyer ya fitar a ranar Litinin, Daily Nigerian ta wallafa.

Ya ce an sheke ‘yan ta’addan yayin wani farmaki da suka kai Forward Operation Base, FOB, da ke Burkusuma, wata iyakar kauye da ke kusa da jamhuriyar Nihar a karamar hukumar Sabon Birni a jahar Sokoto.

“Gagarumin aikin da da dakarun FOB suka yi a cikin watanni da suka gabata a yankin arewa maso yamma ya tada hankulan mayakan ‘yan ta’addan ISWAP da ‘yan fashin daji.”

Daily Nigerian ta rawaito cewa, Sawyer ya sanar da cewa maharan sun zo da yawansu yayin da suke amfani da layikan sadarwa na kasar da ke makwabtaka kuma sun manne a yankunan da babu tsaro sosai.

“Wannan ya faru ne yayin da dakarun suka fita domin ayyukan da aka tura su yankunan.” Ya bayyana cewa, dakarun sun sheke miyagun ‘yan ta’addan masu tarin yawa yayin da suka yi arba.

“Sai dai kuma, a gaggawar da wasu dakarun suka yi wurin kai wa ‘yan uwansu dauki, sun sheke ‘yan ta’addan ISWAP masu tarin yawa, yayin da wasu suka tsere da miyagun raunika.

“Dakarun a halin yanzu sun fattaki miyagun ‘yan ta’addan har zuwa Bassira da ke jamhuriyar Nijar,” yace.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here