Sojojin Najeriya Sun Samo Daliban Makarantar Baptist da ‘Yan Bindiga Suka Sace

Wasu daga cikin daliban da aka sace a wata makarantar Baptist sun kubuta daga hannun ‘yan bindiga.

Wasu sojojin Najeriya ne suka samo su, kuma suka dauko su zuwa cikin gari domin sada su da iyayensu.

A halin yanzu, hukumomin tsaro basu tabbatar da faruwar lamarin ba, amma mazauna sun shaida hakan.

Kaduna – An sake gano wasu dalibai uku da aka sace na makarantar sakandare ta Baptist dake jahar Kaduna.

Sojoji sun gano daliban uku (dukkansu maza) a babban dajin Kankumi da ke karamar hukumar Chikun inda masu garkuwa da mutanen suka yi watsi da su.

Duk da cewa har yanzu rundunar ‘yan sanda ko hukumar makarantar ba su tabbatar da faruwar lamarin ba, amma mazauna yankin sun shaidawa gidan talabijin na Channels cewa daliban uku sun tsere daga hannun ‘yan bindiga.

Bayan sace su daga makarantarsu a ranar 8 ga watan Yuli, an rahoto cewa wasu gungun ‘yan bindiga sun sake sace su yayin da suke yawo a cikin daji.

An ce rukunin ‘yan bindigan na biyu sun sake tattaunawa da iyalansu kuma sun karbi kudin fansa daga iyayen daliban uku, bayan nan suka jefar da su cikin daji kafin daga bisani sojoji suka same su.

Yanzu haka sojoji sun yi wa daliban bayani, kuma za su mika su ga hukumomin makarantar nan ba da jimawa ba.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here