Rundunar Sojojin Najeriya ta Kaddamar da Sabon Atisaye Mai Taken ‘Operation Show No Mercy’

 

Hafsoshin jami’an tsaro sun fara aiwatar da umarnin shugaban kasa Muhammadu Buhari na dakile hare-hare da kashe-kashen da ‘yan ta’adda ke yi.

Rundunar sojojin Najeriya ta kaddamar da sabon Atisaye mai Taken “Operation Show No Mercy wato Atisayen Nuna Wa ‘Yan Ta’adda rashin Tausayi’.

A watan da ya gabata wasu yan bindiga suka kai wa jami’an sojoji kantar bauna a cikin birinin Abuja.

Abuja – Hafsoshin jami’an tsaro sun fara aiwatar da umarnin shugaban kasa Muhammadu Buhari na dakatar da hare-hare da kashe-kashen da ‘yan ta’adda ke yi nan take.Rahoton LEADERSHIP

A jiya ne hafsoshin Rundunar sojoji suka kaddamar da wani Atisaye mai Taken “Operation Show No Mercy wato Nuna ‘Yan Ta’adda rashin Tausayi”.

Shugaban Rundunar Sojan Sama (CAS), Air Marshal Oladayo Amao, ya bayyana haka a wata jawabi da ya fitar a jiya a birnin Abuja.

Ya umurci kwamandojin rundunar sojojin saman Najeriya (NAF) da ke aiki a sassa daban-daban na kasar nan da su ‘nuna rashin tausayi’ tare da yin amfani da karfin wuta a kan ‘yan ta’adda da ke barazana ga tsaro ga al’ummar kasar.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here