Sojojin Najeriya: Ba mu Kashe Kowa ba a Filato Yayin Satar Kayan Abinci
Hedikwatar tsaro ta sojojin Najeriya ta musanta zargin cewa sojoji sun kashe mutum huɗu a Jihar Filato yayin da matasa ke ƙoƙarin wawashe gidan tsohon Kakakin Majalisar Wakilan Najeriya, Yakubu Dogara.
A jiya Juma’a ne jaridar Vanguard ta ruwaito cewa dakarun rundunar Operation Safe Heaven (OPSH) sun halaka mutum huɗu tare da jefa gawarwakinsu a cikin kogi a garin Gwafan da ke Ƙaramar Hukumar Jos ta Arewa.
“Wannan rahoto abin cutarwa ne ga sojojin Najeriya da kuma Operation Safe Heaven, waɗanda suka tabbatar da zaman lafiya a Filato,” in ji hedikwatar tsaron cikin wata sanarwa a yau Asabar.
Read Also:
Sai dai sanarwar ta tabbatar cewa sojojin sun je wurin da abin ya faru kuma har ma sun kama ɓarayin guda 30.
“Saboda dalilai na tarihi, a ranar Lahadi 25 ga watan Oktoban 2020, ‘yan daba sun shiga gidan tsohon kakaki a Lamingo domin yin sata,” a cewar hedikwatar tsaron.
Ta ci gaba da cewa: “Daga baya, dakarun OPSH da ke aikin dawo da zaman lafiya a Jihar Filato da kewaye suka isa wurin domin shawo kan lamarin. Cikin ƙwarewa da bin dokokin aiki, mun kama jumillar barayi 30 a wurin.
“Bugu da ƙari, ‘yan daba 114 aka kama, mata 21 da maza 93, da laifin sata. Idan ba a manta ba sai da aka gabatar da su ga manema labarai.”
An sha zargin rundunar sojojin Najeriya da kisan masu zanga-zangar EndSars da aka kwashe mako biyu ana yi a Lekki Toll Gate da ke Jihar Legas. Sai dai sun musanta zargin, suna masu cewa ba su je wurin ba gaba ɗaya.