Sojojin Najeriya Sunyi Rashin Wani Kwamanda
Kwamanda a rundunar soji ya yanke jiki ya fadi matacce yayin da ya ke tsaka da gabatar jawabi ga sojoji.
Kakakin rundunar soji bai samu damar amsa kiran jaridar Gazette don jin inda aka tsaya dangane da sababin mutuwar babban sojan ba.
‘Yan Najeriya na cigaba da nuna fushi da bacin ransu a kan yadda yakin Boko Haram ke cigaba da zama silar asarar rayukan jami’an tsaro da fararen hula.
Wani Kwamandan soji ya yanke jiki ya faɗi lokacin da ake bada horon yaƙi da ta’addanci,kuma ya rasu jim kaɗan bayan an garzaya dashi asibiti a Maiduguri, kamar yadda jaridar Peoples Gazette ta rawaito.
Read Also:
Laftanar Kanal Isah Yusuf, kwamandan bataliya ta 158 Task force, ya yanke jiki ya fadi da misalin ƙarfe takwas da arba’in 8:40 na safiyar ranar Asabar a daidai lokacin da ya ke yi wa sojoji jawabi a wani ɓangare na bada horon yau da kullum don yaƙar ta’addancin Boko Haram, a cewar majiyarmu.
Ya rasu da misalin ƙarfe tara da arba’in da biyar 9:45a.m ranar Asabar a asibitin sojoji rundunar sojin Najeriya na 7 Division da ke Maiduguri, majiya daga rundunar soji ta faɗi hakan cikin ɓacin rai da alhini ga jaridar Gazette. Har yanzu ba’a kai ga tantance asalin sababin mutuwarsa ba.
Mai magana da yawun rundunar soji yaƙi amsa kira daga jaridar Gazette don jin inda aka tsaya a yammacin ranar Asabar.
Jaridar The Gazette ta gano cewar Hedikwatar soji sun turawa iyalan mamacin saƙon kar ta kwana, sun sanar da su afkuwar lamarin, kafin suzo daga bisani don tura wakilai a hukumance don sanar da iyalan mamacin.
Ƴan Najeriya na cikin fushi sakamakon ayyukan ta’addancin Boko Haram dake cigaba da salwantar da rayukan manya da ƙananan sojoji da sauran al-umma,duk da alƙawuran da hukumomin tsaro da ƴan siyasa keyi na cewar ana gaɓar ƙarshe na kawo ƙarshen yaƙin.