Sojojin Najeriya Sun Samu Nasara Akan ‘Yan Bindiga
Sojojin Najeriya sun samu nasarar mayar da harin ‘yan ta’adda a karamar hukumar Igabi.
Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, Samuel Aruwan ne ya tabbatar da hakan.
Aruwan ya tattauna da shugabannin unguwannin, inda ya shawarcesu da su hada kai da jami’an tsaro.
Sojojin Najeriya sun dakatar da harin wasu ‘yan bindiga a anguwar Sabon Birni da ke karamar hukumar Igabi a cikin jihar a ranar Asabar, 21 ga watan Nuwamba.
Read Also:
Gidan talabijin din Channels, sun ruwaito yadda kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, Samuel Aruwan, ya bayyana hakan.
Kwamishinan ya yaba wa rundunar a kan yadda ta mayar da harin da aka kai. Kamar yadda jaridar Channels ta ruwaito, fiye da mutane 11 ne suka rasa rayukansu a karamar hukumar.
A wannan harin kuwa, sojoji sun shirya musu, inda wasunsu suka tsere da raunuka.
Duk da dai har yanzu mazauna wurin suna cikin matsanancin tashin hankali da fargaba, har suna neman a kara yawan jami’an tsaro a anguwar.
Kwamishinan ya gana da shugabannin anguwar, inda ya rokesu da su hada kawunansu don jami’an tsaro su samu su yi ayyukansu yadda ya dace.