Dakarun Sojojin Najeriya Sunyi Nasarar Kashe Wasu ‘Yan Bindiga
Dakarun sojin Najeriya sun yi nasarar kashe wasu yan fashi da makami.
A wani nasara da suka yi a Benue, an kama yan bindiga biyu sannan aka kwato makamai.
A wani aikin kuma, rundunar sojin Najeriya a sun kuma tarwatsa ayyukan kungiyar Gana a Benue.
A wani yaki da ake da yan bindiga a kasar, rundunar sojin Najeriya sun kashe wasu da ake zaton yan bindiga ne sannan suka samo makamai.
A bisa ga wata sanarwa da Manjo Janar John Enenche, jagoran labarai na ayyukan tsaro, dakarun Operation Whirl Stroke ne suka yi nasarar a ranar Litinin, 21 ga watan Disamba.
Read Also:
Enenche ya ce an kaddamar da aikin ne bayan samun bayanan sirri, inda dakarun suka dauki mataki kan rahoton kasantuwar yan bindiga a wajen wadanda aka alakantada kashe-kashe a Makurdi, babbar birnin jihar Benue.
“An tura dakarun zuwa wajen inda suka hadu tare da gwabzawa a wani musayar wuta. A yayin arangamar, dakarun sun sha kan yan bindigan sannan aka kasha daya daga cikinsu, yayinda wasu da dama suka tsere da raunin bindiga.
“Dakarun sun damo bindigar AK-47 da wani mujalla da harsasai 4.”
Enenche ya kuma ce an kama wasu yan bindiga biyu da suka addabi yankin.
A wani aikin kuma, jagoran labarai na tsaron ya ce dakarun da aka tura jihohin Benue da Taraba sun aiwatar da wani mamaya bayan samun bayanan sirri kan ayyukan sauran yan bindigar kungiyar Gana a karamar hukumar Katsina-Ala.
“Yayinda suke gudanar da kakkaba a mabuyar yan ta’addan, dakarun sun kama wasu yan bindiga biyu da makamansu. An mika yan sandan da aka kama zuwa hukumar da ya dace don daukar mataki na gaba.”