Sojojin Najeriya Sun Raunata Wasu ‘Yan Bindiga

Rundunar OPTS tana samun nasarar ragargazar ‘yan bindiga a jihar Kaduna – Rundunar ta mayar da harin ‘yan bindiga a titin Kaduna zuwa Abuja.

Sojojin sun kuma ragargaji ‘yan bindiga a titin Zaria zuwa Funtua Rundunar Operation Thunder Strike ta mayar da harin ‘yan bindiga da daren Litinin a hanyar Kaduna zuwa Abuja.

An gano yadda ‘yan ta’adda suka tsere cikin daji da raunika saboda sojojin sun hana su cin karensu babu babbaka.

Kamar yadda kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, Samuel Aruwan yace, ‘yan bindigan sun kafa daba wuraren Kakau da shirin harbi, sojoji suka kai musu hari.

“Da rundunar suka gyara cunkoson titin, sai su a gano cewa ‘yan bindiga sun bugi wani direba.

Sannan wasu motoci 2 sun fada daji, saboda tsoron ‘yan bindigan, wanda hakan yayi sanadiyyar jin ciwon wasu fasinjoji da ke cikin mota, jami’an tsaro sun yi gaggawar wucewa da su asibiti.

“Sannan an sanar da gwamnati yadda jami’an tsaro suka ragargaji ‘yan bindiga a titin Zaria zuwa Funtua, a karamar hukumar Giwa da safiyar Talata.

“Sun samu nasarar ceto mutane 2 sannan aka yi gaggawar kai su asibitin koyarwa na jami’ar Ahmadu Bello da ke Shika.

Duk da haka jami’an tsaron suna cigaba da sintiri a wuraren. “Gwamnatin jihar ta tura sakon ta’aziyyar wadanda suka rasa rayukansu, da fatan za su samu rahamar Ubangiji, sannan yana fatan marasa lafiya su samu lafiya da gaggawa,” kamar yadda takardar tazo.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here