Sojojin Saman Najeriya Sun Kawar da Manyan Shugabannin Kungiyar ‘Yan Ta’addan ISWAP da Dama a Jahar Borno.

 

Biyo bayan kai batan jirgin yakin sojin saman Najeriya, sun fatattaki da dama daga cikin ‘yan ISWAP.

Harin ya yi sanadiyyar mutuwar wasu da dama daga ciki har da shugabannin ‘yan ta’addan na ISWAP.

An kuma kwato wasu kayayyaki da suka hada da bindigogi da dama daga hannun ‘yan ta’addan.

A wani kai hari ta sama da kuma amfani da bindigogin atilare, sojojin Najeriya sun kawar da manyan shugabannin kungiyar ‘yan ta’addan ISWAP da dama a jahar Borno.

An kai hare-haren ne ta jiragen sama da ba za a iya tantance su ba bayan mako guda da bacewar jirgin NAF Alpha.

An tattaro cewa harin aka kai kan manyan maboyar ISWAP guda uku a Kusuma, Sigir a Ngala da Arijallamari a cikin kananan hukumomin Abadam, sun kashe shugabanni biyu ‘yan ta’adda Amir Abu-Rabi da Mohamer Likita.

Hakazalika an kashe da kuma masu gadinsu da mayakansu da dama.

Yayin da Abu-Rabi ke lura da karbar haraji a madadin kungiyar ISWAP a yankin Tafkin Chadi, Likita kuwa na cikin kwamandojin da ke kula da hare-hare kan sojojin.

An kai samamen ne a karkashin rundunar sojin sama na Operation Lafiya Dole tare da hadin gwiwar sassan aiki na Artillery na 3, na MNJTF.

Wani jami’in leken asirin soja ya fada wa PRNigeria cewa Kusuma cibiya ce ta shugabannin ISWAP yayin da Sigir da Arijallamari ke a matsayin sansanin horar da ‘yan ta’adda.

Majiyar ta ce: “Wasu daga cikin hare-haren na baya-bayan nan a Damasak, Malam Fatori, Munguno, Dikwa da Marte an hade su ne daga yankunan.

“Hare-hare ta sama da ruwan bama-bamai a kan sansanin ISWAP sun tursasa ‘yan ta’adda da suka tsira da raunuka zuwa yankunan Jibularam da Sabon Tumbu da ke gabar kogi.”

A halin da ake ciki, Sojojin Najeriya tare da tallafin jami’an sa kai na JTF sun yiwa ‘yan ta’adda kwanton bauna a kan hanyar Gubio-Magumeri.

Sojojin sun kafa tarko ne a kauyen Kareram lokacin da suka samu bayanan sirri na ‘yan ta’addan da ke tuka babura da ke tafe daga Kauyen Malam Yaumari don kai hari.

Yayin da aka kashe wasu daga cikin ‘yan ta’addan wasu kuwa sun tsere da munanan raunuka.

Kayayyakin da aka kwato daga hannun ‘yan ta’addan sun hada da manyan makamai da babura da sauransu.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here