Sojojin Ukraine na Samun Galaba Kan Dakarun Rasha – Zelensky

 

Shugaban Volodymyr Zelensky na Ukraine ya ce sojojinsa na samnu galaba wajen nakasa sojojin Rasha da ke kai hari garin Vuhledar da ke Donbas a gabashin kasar.

Ya bayyana yanayin a matsayin mai tsanani, yana mai cewa idan Rasha ta ci gaba da gamuwa da irin wannan koma-baya a yankin da wasu garuruwa irinsu Bakhmut, to hakan na iya gaggauta tabbatar da nasara da kawo karshe yakinsu.

Ukraine na iya kokarinta domin ganin ta hana Rasha sakat ko danna-kai a Donbas yayin da take jiran taimakon sabbin makamai da kasashen yamma suka yi mata alkawari.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here