An Soki Kalaman Shehu Sani Kan Goyan Bayan Dakatar da Fubara
FCT, Abuja – Bayan dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara na Jihar Rivers, Sanata Shehu Sani ya bayyana cewa dokar ta-baci ita ce kadai mafita don dawo da zaman lafiya a jihar.
Sai dai matasa sun yi rubdugu ga Sanata Shehu Sani suna kalubalantar ra’ayin da ya bayyana a matsayinsa na dan gwagwarmaya.
A cikin sakon da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Shehu Sani ya ce an yi kokarin warware rikicin ta hanyar shari’a, siyasa, har ma da hanyoyin addini, amma hakan ya ci tura.
Shehu Sani ya kare matakin Tinubu
Sanata Shehu Sani ya bayyana cewa matakin Shugaba Tinubu na kafa dokar ta-baci a Jihar Rivers shi ne kadai hanyar tabbatar da zaman lafiya.
Ya ce rashin samar da mafita ta hanyoyin shari’a da siyasa ya sanya dole a dauki matakin gaggawa domin kare martabar jihar.
A cewarsa, Jihar Rivers tana da matukar muhimmanci ga ci gaban tattalin arzikin Najeriya, don haka ba za a bar rikicin ya ci gaba ba.
Read Also:
Matasan sun yi rubdugu wa Shehu Sani
Wani matashi, Abdulaziz A. Galadima, ya soki matakin, yana mai cewa gwamnatin tarayya ba ta taba neman sahihin mafita ba.
Matashin ya yi zargin cewa:
“Ana amfani da dokar ne kawai don tabbatar da mulkin mallaka a Jihar Rivers, ba don dawo da doka da oda ba.”
Shi ma Yusuf Isa ya ce:
“Idan rikicin ‘yan bindiga da masu tayar da kayar baya ba su sa gwamnati ta kafa dokar ta-baci ba, amma hare-haren bututun mai suka haddasa hakan,
“To a fili take cewa mulkin Tinubu yana fifita bututun mai da muradin Wike fiye da jin dadin jama’a.”
Umar Saeed Yushau ya mayar da martani ga Sanata Shehu Sani da cewa:
“Je ka nemi wadanda za ka yaudara, ba mu ba.”
Shi ma Adam Nasir Uthman ya yi martani wa Shehu Sani da cewa:
“Da ace kana a dayan bangaren siyasar, (‘Cikin ‘yan adawa) da wata maganar daban za ka yi.”
Bashir Lamido ya bayyana cewa dakatar da Gwamna Fubara da sauran jami’an gwamnati da barin Nyesom Wike yana nuna cewa akwai son rai a matakin.