Dakarun Somaliya Sun ƙwato Gini Daga Hannun Mayaƙan Al-Shabab
Kafofin yaɗa labaran Somaliya sun ce dakarun ƙasar sun yi wa wani ginin gwamnati a tsakiyar birnin Mogadishu ƙawanya, domin kawo ƙarshen mamayar da mayaƙan al-Shabab ta yi wa ginin.
Lamarin ya fara ne da harin bom a cikin wata ƙaramar mota a kofar shiga ginin a gundumar Hamarweyne, kafin daga bisani mayaƙan waɗanda suka ɓatar da kama a matsayin sojoji su mamaye ginin.
Read Also:
Ma’aikatar yaɗa labaran ƙasar ta ce jami’an tsaro sun samu nasarar kuɓutar da duka ma’aikatan da ke cikin ginin, tare da kashe mayaƙan al-Shaban shida a ƙoƙarin kwato ginin.
Kafofin yaɗa labarai masu alaƙa da ƙungiyar sun ambato mai magana da yawun ƙungiyar na cewa sun kashe ma’aikatan gwamnati 34.
A shekarar 2019 ƙungiyar al-Shabab ta kai harin ƙunar bakin wake a kan ginin tare da kashe magajin birnin na wancan lokaci Abdirahman Omar Osman.